Hikaya: Kowa Ya Yi Da Kyau

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Hikaya: Kowa Ya Yi Da Kyau, Zai Ga Da Kyau


Gabatarwa

Wata rana, wata tururuwa ta fita kiwo, bayan ta yi kiwon ta, sai ta tafi bakin kogi domin ta sha ruwa sannan kuma ta huta gajiyarta. Da isar ta bakin kogi sai ta kafa kanta a bakin gaɓar kogi ta fara shan ruwa, tana cikin shan ruwan nan, sai ƙafarta ta zame, ta faɗa cikin kogi. Ita kuma tururuwa bata iya ruwa ba balle ta fice. Saboda haka tana-ji-tana-gani, ta fara nutsewa.

Ashe duk lokacin da waɗannan abubuwa ke faruwa da wannan tururuwa, akwai wata kurciya da ke kan wani dutsen da yake a cikin ruwan tana kallon ta. Saboda haka sai kurciyar nan ta ɗauki ciyawa ta garzayo da gudu, ta tafo aikin ceto. Tana zuwa bata yi watawata ba, sai ta jefa wannan ciyawa a gaban tururwar nan. Da tururuwa ta ga wannan ciyawa sai ta ɗafe. Tana ɗafewa, sai kurciyar nan ta yi caraf, ta tsamo ciyawar nan daga cikin ruwa ta kai kan tudu ta jefar, ta koma gidanta da ke kan dutse a cikin ruwa. Ita kuma tururuwa ta samu kanta, ta koma gida.

A kwana-a-tashi, wata rana sai kurciyar nan ta tafi kiwo ita ma. Da ta yi kiwonta, ta gaji, sai ta haye kan reshen wata bishiya tana hutawa. Can sai ga wani marhabi ya sanɗo saɗaf, saɗaf ta bayan kurciyar nan, sai da ya zo daf da ita ya tsaya, ya gyaggyara bindigarsa, ashe duk abin da ya ke yi, tururuwar nan tana kallon sa. Ita ma tururuwar nan da ta ga haka, sai ta garzayo ta ɗafe agarar marhabin nan don ta yi aikin ceto. Bayan maharbi ya gama seta bindigarsa don yin harbi, sai ya matsa kunamar bindigar nan zai harbi kurciya, ai kuwa da tururuwar nan ta ga haka sai ta girya masa cizo, sai marhabin nan ya firgice ya saki bindigar nan. Yana sakin bindigar sai ta yi ƙara durum, jin wannan ƙara sai ya sa wannan kurciya ta fita da gudu sai gida. Wannan shi ne sakamakon kyakkyawan aiki. Saboda haka kowa ya yi da kyau, zai ga da kyau.


Ana iya turo labari domin a wallafawa ta:
Was-af: 0803 964 8244 (+234803 964 8244)
Imel: rumbunilimi@gmail.com


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub