Hikaya: Ladabi

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Hikaya: Ladabi Tushen Nasara


Gabatarwa

A wani gari an yi wani attajiri, yana son ya ɗauki ma'aikacin da zai riƙa yi masa rubuce-rubuce a kantinsa, kuma yana son wannan ma'aikaci ya zama saurayi ne kuma mai gaskiya. Saboda haka sai ya bayar da sanarwa, ya kuma saka rana da lokaci. Kantin nasa ne ya zama gurin ganawa.

Da ranar ganawar ta zo, samari da yawa suka yi cincirindo a ƙofar kantin nasa, saboda haka sai ya fara ganawa da su ɗaya-bayan-ɗaya, yana yi musu tambayoyi suna amsa masa. Hikimar yin hakan ita ce ya samu saurayi mai gaskiya wanda zai iya riƙe masa amana. Ana tsaka da wannan ganawa, sai Allah ya datar da shi da wani saurayi mai hankali. Bai ma ɗauki lokaci mai tsawo ba wajen tantance wannan saurayi. Da maƙwabcinsa ya lura da rashin daɗewar wannan saurayi yayin ganawar su da attajirin nan kuma gashi shi ya zaɓa, sai ya tambaye shi ya aka yi ya tantance wannan saurayi cikin ƙaramin lokaci?

Sai ya amsa masa da cewa, na lura da wasu halaye nagari tare da shi. Farko, da zai shiga kantin, ya goge takalminsa a kan shinfiɗar goge takalmi da ke bakin ƙofa, ya kuma rufe ƙofar a hankali, abin da ke nuna cewa shi mai tsafta ne kuma mai tsari; sannan ya gabato ni da sallama, ya kuma yi magana da ni cikin nishaɗi da girmamawa, sai na fahimci cewa yana da kyakkyawan ladabi; ya zauna yana mai kallon gabansa ba tare da damuwa da abubuwan da ke gudana a wajen ba, sai na fahimci cewa shi mai ƙasƙantar da kai ne. To, a duk lakcin da ka samu mutumin da ya tattara waɗannan halaye, to haƙiƙa ya ɗara saura.


Ana iya turo labari domin a wallafawa ta:
Was-af: 0803 964 8244 (+234803 964 8244)
Imel: rumbunilimi@gmail.com


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub